BORNO: Sama Da Mayakan ISWAP 104 Da ‘Yan Uwansu Sun Mika Wuya

Akalla mayakan kungiyar ISWAP 104 na lardin Yammacin Afirka, sun mika wuya ga sojojin Najeriya a jihar Borno.

WASHINGTON DC — Hedikwatar rundunar sojin Najeriya ta bayyana hakan ne yau Litinin ta wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

A cewar sanarwar, wadanda suka mika wuya ga rundunar ta 25 Task Force Brigade Damboa sun hada da maza 22, mata 27 da yara 55.

Sanarwar ta ce, “ISWAP da iyalansu da adadin su ya kai 104, da suka hada da maza 22, mata 27 da yara 55 sun mika wuya ga dakarun ta 25 Task Force Brigade Damboa, jihar Borno a ranar Asabar 5 ga Fabrairu 2022.”

Rahotanin na cewa iyalan ‘yan ta’addar ISWAP na ficewa daga Marte sakamakon mumunar farmakin da sojoji suka kai musu.

-source:VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.