Cikin sansanin tsare ƴan IS a Syria, jami’ai sun ce tashin hankali da tsattsauran ra’ayi matsala ce da ke ci gaba da ƙaruwa.
Sansanin al-Hol wuri ne da yake a rikice da mutane cikin wani mawuyacin hali da kuma haɗari.
Sansani ne da yake zaman gida ga mata da ƴaƴan mayakan kungiyar IS.
Birni ne mai tanti-tanti inda iyalai suke a gwamutse, ga kuma jami’an tsaro dauke da makamai da ke zagaye da su, wasu na kan dogayen hasumiyoyi da ke sa ido a kansu baya ga waya mai tsini da aka killace sansanin, duk domin a tabbatar suna tsare.
Tafiyar sa’a hudu ce a mota zuwa katafaren sansanin da ke a yanki na hamada daga al-Malikyah, a wuce birnin Qamishli, zuwa kusa da iyakar Syria da Turkiya a arewa maso gabashin Syria.
A cikinsa, mata za ka gani sanye da bakaken kaya da niƙabi, wanda ba ka iya ganin komai sai idanunwansu – wasunsu na nesa-nesa da mutane ba fara’a wasu kuma ga su nan da ka gansu ma kai ba za ka iya kusantarsu ba saboda fushi da barazana.
Sai dai can a gefe daya a kusa da wata kasuwar sayar da kayan lambu, akwai wasu tarin mata da suke kare kansu daga rana wadanda su kuma a shirye suke su amayar da abin da ke ransu su yi magana. Sun je ne daga gabashin Turai.
Na tambaye su yadda suka samu kansu a nan, sai dai sun yi min dan bayani ne kawai, suna dora alhakin a kan mazajensu kan yadda suka yi wannan tafiya mai dinsa, suka shiga kungiyar IS tare da zama a karkashin kungiyar da ke azabtarwa da gana akuba tare da bautar da dubban mutane.
Laifinsu daya kawai shi ne, kamar yadda suka kafe a kai shi ne, soyayya da mutanen da ba su dace da su ba.
Wannan kusan labari ne da aka sani da ake ji daga matan mayakan IS, inda suke kokarin nesanta kansu daga gwamnatin kungiyar da ta aikata ta’addanci wadda kuma manufarta a bayyane take.
Mazajensu ko dai sun mutu ko an daure su ko sun bata, yanzu kuma ga su nan a tsare tare da ƴaƴansu.
Kusan mutane dubu 60 ke tsare a nan, wadanda suka hada da iyalan mayakan kungiyar IS na kasashen waje su 2,500. Yawancinsu sun kasance a wannan sansani tun lokacin da aka murkushe mayakan masu ikirarin jihadi a Baghuz, a 2019.
Matan suna magana ne a hankali suna tsoron kada su ja hankali da za su jefa kansu cikin wani hadari ko ma rasa ransu.
Ba wai masu tsaron nasu suke jin tsoro ba, suna tsoron sauran matan ne, masu tsattsauran ra’ayi wadanda har yanzu suke sanya dokoki a sansanin.
A cikin daren da muka je sansanin an samu wata mata da aka kashe.
Kisan da ake yi kullum
Tashin hankali da tsattsauran ra’ayi a sansanin babbar matsala ce ga dakarun Syria na Democrtic Forces wadanda Kurdawa ke jagoranta, da suke tafiyar da sansanin.
Dr Abdulkarim Omar, wanda kusan ke rike da mukamin ministan waje na hukumar da Kurdawa ke jagoranta a yankin arewa maso gabashin Syria, ya amsa cewa IS ce ke mulki har yanzu a sansanin na al-Hol.
Ya ce mata masu tsattsauran ra’ayi su ne ke da alhakin tashin hankali da ta’addanicin da ake gani a sansanin.
Ya ce, “Akwai kashe-kashe a kullum, sukan kona daki ko tantin wadanda ba sa bin akidar IS, kuma suna koyar da wadanan tsaurararan akidu ga ƴayansu.”

Akwai yara kusan a ko’ina, wadanda iyayensu suka kai su Syria daga Asiya da Afrika da Turai domin su zauna a karkashin IS.
Babu wani abu takamaimai da za su yi. Wasu daga cikin yaran sun rika jifanmu da duwatsu a lokacin da motarmu ke wucewa ta bangaren ƴan kasashen waje na sansanin, har ma gilashin tagar motar ya fashe.
Masu tsaron lafiyarmu da ke cikin motar ko gezau ba su yi ba domin abu ne da suka saba gani.
Wasu yaran kuwa ba abin da suke yi, in ban da kallonmu kawai suna zaune a kofar tantinsu. Yawancinsu ba irin tashin hankalin da ba su gani ba, saboda yadda IS ke ta kokarin kare yankunanta da mayakanta da ke tafiya daga nan zuwa can a fadin Syria da Iraqi.
Da yawansu ba abin da suka sani sai yaki kumaa ba su taba zuwa makaranta ba.
Wasu suna da raunuka a jikinsu da ake gani. Na gan wani yaro da aka yanke masa kafa, yana tafiya a kasa a tarin rerayi.
Dukkaninsu sun rayu cikin akuba da rashi, domin kusan yawancinsu wani ya rasa uwa ko uba.

Domin magance tashin hankalin da ake yawan samu yau da kullum a sansanin, akwai matakan da ake dauka kullum na tabbatar da tsaro. Amma fa ba shi ke nan ba akwai wasu.
Ana daukar manyan yara a matsayin barazana a wurin. Da zarar sun balaga sai a kwashe su a kai su wasu cibiyoyin masu tsaro nesa da iyaye da ƴan uwansu.
Dr Omar ya ce , “Idan suka kai wasu shekaru, sukan zama hadari ga kansu da wasu, saboda haka ba mu da zabi da ya rage illa mu gina cibiyoyin gyara tunanin yaran nan.”
Ya ce suna ganawa da uwayensu mata ta hanyar kungiyar Red Cross (ICRC).
‘Kullum yana kara girma‘
Arewa da al-Hol, akwai wani sansanin na Roj, wanda karami ne, da shi ma yake dauke da matan mayakan IS da yara. A nan ba a samun tashin hankali sosai. A nan ne yawancin mata ƴan Birtaniya da suka hada da Shamima Begum da Nicole Jack tare da ƴaƴanta mata suke zaune.
An raba sansanin ne da danga ta waya. Na hadu da wasu mata daga tsibirin Karebiya (Caribbean) na Trinidad and Tobago, wanda daya ne daga cikin wuraren da suke da mayakan IS masu yawa daga yankin Amurka ta arewa da latin Amurka.
Wata matar tana da yaro mai shekara. Ta kai ƴaƴanta domin su zauna a karkashin IS, kuma bayan da aka kashe mininta, sun ci gaba da zama a karkashin kungiyar ta IS har zuwa karshe.
Ta ji yadda ake ware yaran da suka girma daga inda iyayensu suke saboda haka hankalinta ya tashi yanzu za a iya yi mata haka, a raba ta da ƴaƴanta.
Kullum dan nata yana kara girma, ita kuma tana kara damuwa.
A kusa da mu ga yaran nan yana wasan kwallon kafa da kannensa maza da mace. An kashe babansu ne a wani harin sama. ya gaya min cewa zai yi kewar mahaifiyarsa idan aka dauke shi daga wurinta.

Tsafta a nan tana da muhimmanci, akwai bandaki na wuri-wuri a sassan sansanin da wuraren wanka, kuma ana samun ruwan sha daga tankuna, wanda wannan abu ne da dukkanin yarn suke kokawa a kai.
Akwai wani dan karamin sasahe da ke zaman kamar kasuwa inda ake sayar da kayan wasan yara da abinci da tufafi.
A kowa ne wata ana ba iyalai kayan abinci, da tufafi na yara. Wasu na zaune a tantunan da suke na iyalai masu yawa.
A karkashin IS wasu daga cikin matan kadan suna auren namiji daya, to irin wannan zama na tare ya ci gaba har yanzu inda suke zaune tare suna raba ayyukan kula da yara da na gida a tsakaninsu.
Ɓarna, ruwan bama-bamai, yaƙi
Yara da yawa suna halartar makarantar wucin-gadi wadda kungiyar agaji ta Save the Children ke tafiyarwa.
“Muna jin labarai da yawa kuma abin takaicin ba wani daga cikin labaran nan da yake mai dadin ji ne, amma fatanmu shi ne su koma gida su yi rayuwa ta yara cikin walwala da koshin lafiya da kwanciyar hankali,” in ji Sara Rashdan, ta kungiyar ta Save the Children daga Syria.
“Mun ga sauyin dabi’a da yawa. A da muna ganin suna zanen hotunan barnar hare-hare, da ruwan bama-bamai da yaki, amma yanzu zanen abubuwa suke yi masu kyau, na farin ciki da furanni da gidaje.”
Sai dai ba mu san yadda wadannan yara za su fita ba ko kuma yadda rayuwarsu za ta kasance a gaba ba.

Wasu kasashen yammacin duniya na kallon matan mayakan IS na kasashen waje a matsayin barazana ga tsaro.
Da yawa daga cikin mata sun musanta cewa su barazana ne ga tsaro. Amma kuma duk da haka ba sa son magana a kan abin da ya shafi wadanda IS ta kashe ko muzantawa, kamar dubban mata yan Yazidi wadanda IS ta mayar bayi ko kwarkwarori da sauran ire-iren wadanda ke yakar kungiyar da ta yi wa kisan gilla. Ko kuma wadnda ta dauka makiya ne ta rika azabtar da su ko datse musu kai, kisa na mugunta.
Wannan daman abu ne da wadanda suka shiga IS suka saba yi.
Ba su san abin da ke faruwa a sassan duniya ba, kuma yan kadan ne daga cikinsu suka san yadda ake daukarsu a kasashensu.
Wasu daga kasashen Turai kamar Sweden da Jamus da Belgium suna kwashe wasu daga cikin yaran da iyayensu mata.
Kuma yadda yanayi yake kara tabarbarewa a sansanin hukumomin Kurdawa na kira ga karin kasashe da su debe ƴan kasarsu su mayar da su gida.
“Matsala ce ta duniya amma kasashen duniya sun ki mayar da hankali a kanta, kuma idan abin ya ci gaba a haka za mu fuskanci bala’in da ya fi ƙarfinmu” in ji Dr Omar.”
-Source: BBCHausa-