Atiku Ya Zabi Okowa A Matsayin Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa A PDP

Kafin ya zama gwamna, Okowa Sanata ne a majalisar Dattawan Najeriya inda ya wakilci arewacin jihar Delta karkashin jam’iyyar ta PDP.

WASHINGTON D.C. — Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi A. Okowa a matsayin abokin da zai taya shi takara.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis yana mai nuna farin cikinsa da zabin Okowa.

“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Gwamna Ifeanyi A. Okowa ne abokin takarata.” Atiku ya ce.

Hukumar zabe ta INEC ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasar kasar nan da ranar 17 ga watan Yuni, a matsayin wa’adi da za su gabatar da dukkan ‘yan takararsu na mukamai daban-daban da mataimakansu.

Sa’o’i kafin cikar wa’adin, jam’iyyar ta PDP ta kafa wani kwamiti mai dauke da mambobi 17 don tantance Okowa a ranar Alhamis.

Dan shekara 63, Okowa na wa’adin mulkinsa na gwamna na karshe a jihar ta Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Kafin ya zama gwamna, Okowa Sanata ne a majalisar Dattawan Najeriya inda ya wakilci arewacin jihar Delta karkashin jam’iyyar ta PDP.

Asalinsa dan kabilar Ika ne daga yankin Owa-Alero da ke jihar ta Delta mai arzikin mai.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.