‘Yan Sandan Yankin Ashantin Ghana Na Jinjinawa Aikin Su

Duk da alamomin karuwan miyagun ayyuka a Ghana, rundunar ‘yan sandan yankin Ashanti tana yabawa kanta a kan nasarorin da ta samu wurin yaki da miyagun ayyuka.

Jami’an ‘yan sanda na yankin suna matukar farin ciki da nasarar da suka samu wurin kame da gurfanar da wasu da ake zargin miyagu ne dake ayyukan ta’addanci a yankin Ashanti.

Mukaddashin kwamishinan rundunar ‘yan sandan Ashanti, DCOP David Agyemang Adjem wanda ya ambato jerin kame-kame masu muhimmanci wurin dakile miyagun ayyuka, ya ce kokarin ‘yan sandan na yin tasiri, ganin yanda yankin ya samu ragowar miyagun ayyuka tun daga cikin shekarar 2020.

“A bara da ma bana, ayyukan ‘yan bata gari bai yi muni kamar yanda aka saba gani ba idan aka kwatanta da kididdigar baya. Sai dai akasi da aka samu, sune miyagun ayyuka kalilan amma masu tsananin muni da tashin hankali sun faru,” inji shi.  

Yankin Ashanti ya samu hari a kan motar daukar kudin bankuna sau biyu a wannan shekara, lamarin da ya kai ga mutuwar ma’aikacin banki da kuma dan sanda. Gungun maharan sun kashe General Lance Corporal Martin Baba dake yiwa motar kudin rakiya daga garin Dunkw-On-Offin zuwa bankin Ghana Commercial Bank reshen New Edubiase.

‘Yan sanda sun ce wani dan shekara 22 wanda ya gama karatun sakandare mai suna John Appiah, da ake yiwa lakabi Omega shine ke jagorantar ‘yan bindigan kana a halin yanzu ya arce ana neman sa.

DCOP Agyemang Adjem ya ce binciken ‘yan sanda na amfani da tsohon tsarin binciken kwakwaf da na zamani da wasu dabaru domin kamo miyagun da kuma gurfanar da su gaban doka.

Rundunar ‘yan sandan yankin Ashanti sun kara kaimi wurin aikin sa ido a cikin unguwanni a yankin.

-Source: Myjoyonlne-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.