Ana Zargin Wani DPO Da Yin Amfani Da Tabarya Wajen Azabtar Da Mutane

A Najeriya batun zargin jami’an tsaro da cin zarafin Bil-Adama ya zama ruwan dare, domin kuwa kusan kowace rana sai an sami rahoton ire-ire na cin zarafin mutane da suka hada har da duka, gallazawa, wani lokacin har ta kai ga an rasa rayuka.

WASHINGTON, D.C. —  A jihar Bauchi an zargi wani DPO din ‘yan Sanda, da ke ofishin ‘yan Sanda na Township da azabtar da wasu matasa guda uku, bisa zargin satar kaji guda 7, wanda biyu daga cikin matasan suka mutu, a yayin da dayan kuma ya karye a kafafuwansa.

Binciken ya nuna cewar DPO din mai suna, SP Baba Muhammed ya yi kaurin suna wajen azabtar da mutane ta hanyar duka da tabarya, kamar yadda abokin yaran biyu da suka mutu, mai suna Abdulwahab Bello, wanda shi kuma yarasa kafafuwansa ya shaidawa wakilin Muryar Amurka.

Daya daga cikin mahaifiyar da dan nata ya mutu a hannun ‘yan sanda ta ce, ita tana son a bi mata kadin danta da aka kashe. Kuma ta ce, ya kamata hukuma ta yi abin da ya dace.

An gurfanar da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, da DPO din da ake zargi SP Baba Muhammed gaban babban kotun tarayya da ke Bauchi, a cewar lauyan da ya shigar da karar.

Hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta yi bayani a hukumance kan batun, DSP Muhammed Wakil shi ne kakakinta inda ya ce, kwamishinan ‘yan sanda ya kafa kwamitin da zai yi binciki, kuma duk dan sandan da aka kama da cin zarafi, hukumar za ta hukuntashi.

A halin da ake ciki dai gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin binciken duk wani lamari na zargin cin zarafin bil adama da jami’an ‘yan sandan SARS ke aikatawa karkashin babban mai sharia, Habibu Idris Shall.

-Source:VOAHausa-

One thought on “Ana Zargin Wani DPO Da Yin Amfani Da Tabarya Wajen Azabtar Da Mutane

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.