Ana zaben ra’ayin hukunta tsoffin shugabannin Mexico

A yau ‘yan kasar Mexico ke zaben raba-gardama, kan bukatar da shugaban kasar Andres Manuel Lopez Obrador ya gabatar kan ko ya kamata a binciki tsoffin shugabannin kasar a kan laifukan da suka yi a zamanin mulkinsu.

Shugaban wanda ya ce shi ba zai kada kuria’a a zaben na rafaranda ba duk da shi ne ya bullo da bukatar, ya ce shugabannin na baya sun rika tafka ta’asa san ransu.

Sai dai masu sukarsa sun ce kuri’ar wani yunkuri ne na neman suna, da kuma neman kawar da hankalin jama’a daga shugaban da suke gani na neman zama dan kama-karya.

Ba shakka, tsarin shari’a na Mexico, yana matukar bukatar sauye-sauye na gaske a ra’ayin yawancin ‘yan kasar, domin a fagen siyasa ana tafiyar da abubuwa son rai, ba bincike, kusan ba a hukunta manyan masu iko ko jami’an gwamnati kuma cin-hanci da rashawa sun zama ruwan-dare.

Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador ya gabatar da wannan zabe na jin ra’ayin jama’a ne a matsayin wani mataki na gagarumin sauyin da yake son kawowa don yaki da rashawa, da kuma ganin an hukunta da dama daga cikin shugabannin kasar na baya kan laifukan da suka tafka.

Masu suka na ganin Shugaba Andrés Manuel López Obrador na neman suna ne kawai da shirin

Sai dai masu sukar shugaban na ganin kuri’ar ba komai ba ce illa wani abu na burga da neman suna a siyasa kawai, da tamkar wasan kwaikwayo ne.

A yanzu dai a dokokin kasar ta Mexico babu wata doka da ta hana gurfanar da tsoffin shugabanni gaban kotu a kan duk wani laifi da ake zargi sun aikata.

Saboda haka idan har da gaske yake ko kuma yana son bincikensu to da sai ya tafi gaba-gadi ya kaddamar da tuhuma a kan tarin zargin da ake musu.

Hatta ita kanta kotun kolin kasar ba ta zartar da cewa ko ita wannan kuri’a ma tana da muhalli a tsarin mulkin kasar ba.

Ssaboda haka kusan ita ma kotun ta rage wa kuri’ar karsashi ga masu zaben, abin da daman masu suka suka ce ba shi da wani muhimmanci.

A takardar kuri’ar an tambayi mai zabe ne: ”Shin ka yarda ko kuma ba ka yarda ba, a dauki matakin da ya dace, bi sa tanadin tsarin mulki da sharia’a domin fayyace hukuncin da jagororin siyasa suka dauka a baya domin tabbatar da adalkci da kuma ‘yancin wadanda aka ci zarafi.”

One thought on “Ana zaben ra’ayin hukunta tsoffin shugabannin Mexico

Comments are closed.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.