Ƙwararru kan harkar tsaro a Najeriya sun yi kira ga hukumomin ƙasar su fara yin ƙoƙarin magance rashin yardar da ta yi katutu a tsakanin ‘yan ƙasar da nufin daƙile yawan kashe-kashen mutane da ake fama da shi.
Sun kuma bukaci hukumomi su ɓullo da matakan inganta tsarin zamantakewar da ya taɓarɓare musamman a arewacin Nijeriya da kuma tabbatar da hukunci ga masu aikata laifuka a kasar.
Wannan wani ɓangare ne na rahoton da wani kamfanin tsaro wato Beacon Consulting Company ya fitar inda ya tattara alƙaluma na kashe-kashen da aka samu a watan Satumban da ya wuce.
Shugaban kamfanin Kabiru Adamu, ya shaida wa BBC cewa rahoton ya nuna cewa an kashe mutum 663 a watan Satumba kadai a sassan Najeriya daban-daban.
Ya ce alƙaluman sun haɗa da yawan mutanen da aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma na ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ma waɗanda jami’an tsaro suka kashe a bakin aiki, da kuma su kansu jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a fagen daga.
- Coronavirus a Najeriya: Ana duba yiwuwar sake kafa dokar kulle a wasu yankunan kasar
- Ana zaben ra’ayin hukunta tsoffin shugabannin Mexico
Kabiru Adamu ya ce kusan watanni uku kenan tun daga watan Yuni ake samun irin wannan adadi, kamar yadda bincikensu ya gano.
Ya kuma kara da cewa matakan da wasu gwamnonin arewa maso yamacin kasar suka dauka wajen yaki da ‘yan bindiga sun ba wa gwamnatocin damar aiwatar da manufofinsu, sai dai akwai bukatar neman shawarwarin kungiyoyi irin nasu, don tabbatar da ikirarin da ake yi na cewa ana samun nasara a kansu.
”Dazuzzukan da ƴan bindigar nan ke bi sun ratsa jihohi da dama, don haka idan ba a dauki matakin bai daya, da kuma hada guiwa ga kasashe maƙwabta ba zai yi wuya a iya magance matsalar baki ɗaya’ inji shi
Shugaban kamfanin nan Beacon Consulting ya ce rashin shigar da majalisun dokokin jihohin da aka sanya dokokin ya sa suna ganin cewa an yi wa Dimukradiyya karan tsaye.
-Source: BBCHausa-