Akwai Yiwuwar Kara Farashin Kiran Waya Da Shiga Yanar Gizo A Najeriya

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta ce tana gudanar da wasu sauye-sauye a kan ayyukan gudanarwar kamfanonin sadarwa da kudaden da suke biya a kowacce shekara a kasar.ABUJA, NIGERIA. — 

A cikin sauye-sauyen da hukumar ta NCC ke kan gudanarwa har da duba farashin ayyukan da kamfanonin sadarwa a kasar ke samarwa ga ‘yan kasa.

Hukumar ta ce tana wadannan sauye-sauyen ne domin daidaita gudunmawar da ayyukan sadarwa ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin kasa don bin sahun takwarorin ta na kasashen duniya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin jawabin da shugaban hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ya yi, a lokacin wani taron jin ra’ayoyin ‘yan kasa da ya gudana a birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

Wasu majiyoyi daga hukumar sun yi nuni da cewa, da zarar NCC ta kammala aikin sauye-sauyen da ta ke kai a halin yanzu, akwai yiwuwar farashin kudin kira da na shiga yanar gizo su karu a kasar.

Wannan mataki na baya-bayan nan da hukumar sadarwa ta dauka na sauye-sauyen, ya ci karo da sanarwar yiyuwar raguwar farashin kiran waya da amfani da yanar gizo da kashi 65 cikin 100 da maitaimakin shugaban Najeriya ya sanar a ranar 25 ga watan Yuni a yayin wani taro.

Farfesa Yemi Osinbajo, a wancan lokacin ya bayyyana cewa gwamnati na wani gaggarumin aiki na tabbatar da rage farashin shiga yanar gizo a kasar, shirin da ya ce zai rage farashin kowanne gigabait daya da kusan kashi 70 cikin 100, ta yadda farashin ba zai wuce naira 390 ba nan da shekara 3 masu zuwa, domin saukaka shiga yanar gizo ga ‘yan kasar.

Masani kan sha’anin fasahar zamani da kuma yanar gizo, Yusufudeen A. Yusuf, ya ce wannan rashin daidaito a tsakanin bangarorin gwamnati na cimma matsaya a kan ababen da suka shafi kasa ba abu ne mai kyau ba, inda ya yi kira ga gwamnatin kasar ta hada kai domin cimma nasara a ayyukan ci gaban kasa.

Duk kokarin jin karin bayani game da wannan lamarin daga bakin hukumar NCC ya ci tura bayan taron.

-Source: VOAHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.