Afghanistan: Limamin Yahudawa da ke taimaka wa ‘ƴan Afghanistan tserewa daga Taliban

Labarin wasu yara huɗu ne da ke guje wa mulkin ƙungiyar Taliban a birnin Kabul na Afghanistan ya sa wani malamin Yahudawa daga birnin New York na Amurka ya ɗauki waya ya yi wani kira mai muhimmancin gaske.

‘Yan kwanaki bayan haka, mazauna Afghanistan suka fara tururuwa zuwa filin jirgin sama na Kabul da zummar barin ƙasar ta kowane hali bayan Taliban ta ƙwace iko da ƙasar ranar 15 ga watan Agusta.

“Na yi ta tunani game da yaran nan huɗu waɗanda dukkansu ‘yan ƙasa da shekara 18 ne cewa ko suna raye, dole na yi ƙoƙari na kai musu ɗauki,” kamar yadda Rabbi Moshe Margaretten mai shekara 41 ya faɗa wa BBC.

Bayan ya gano cewa mahaifiyarsu ta fice daga Afghanistan zuwa Amurka bayan mahaifinsu ya ɓace – inda ta bar yaran tare da ‘yan uwanta – sai ya bi sahun lauyan da ke kare su.

“Na faɗa mata cewa ki yarda da ni, ina ganin zan iya taimaka wa yaran nan su kai ga filin jirgi.”

Dalilin da ya sa ba zai yiwu a ƙi ɗaukar mataki ba

Maƙasudin abin da Rabbi Margaretten yake so ya cimma shi ne haɗa yaran da mahaifiyarsu, abin da ya ce yana so ya cimma cikin gaggawa.

Ta hanyar gidauniyarsa mai suna Tzedek Association da kuma wata ƙungiya da ke yankin, ya ɗura ɗammarar fita neman su.

“Mun sa mutanenmu su bai wa yaran kulawa kuma awa ɗaya bayan haka sai ga su a cikin filin jirgin,” in ji shi. Ya ƙra da cewa cikin ‘yan awanni sai ga su a kan hanya zuwa Qatar, kafin daga bisani su isa Amurka.

Ya ce ya kaɗu sosai lokacin da ya ga yaran na haɗuwa da mahaifiyar tasu.

Rabbi Margaretten tare da yaran huɗu da ya taimaka wa suka tsere daga Afghanistan lokacin da suka haɗu da mahaifiyarsu

Ƙungiyar malamin ta ce ya zuwa yanzu ta taimaka wa gomman masu fafutika da alƙalai waɗanda suka yi aiki tare da tsohuwar gwamnatin Afghanistan da ta Birtaniya da kuma dakarun Amurka a ƙasar.

“Ya aka yi malamin Yahudawa daga Brooklyn, Amurka yake taimaka wa Musulmai a Afghanistan? Amsar mai sauƙi ce,” a cewarsa, “iyayena da kakannina dukkansu sun tsira daga kisan ƙare-dangi da aka yi wa Yahudawa”.

Malamin wanda iyayensa suka fito daga ƙasar Hungary, ya ce tashin hankalin da danginsa suka shiga lokacin kashe-kashen da jam’iyyar Nazi ta mamaye Turai a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu – da kuma yadda lamura ke faruwa a Afghanistan – su ne suka sa ya ga cewa ba zai yiwu ya ƙyale ba, ba tare da ɗaukar mataki ba.

“An tilasta wa iyayenmu neman tsira da rayuwarsu kuma sun fuskanci irin wannan tashin hankalin,” in ji shi.

Rabbi Margaretten ba shi da wata alaƙa da Afghanistan kafin ya samu aiki da wani ɗan kasuwa Bayahude, Zablon Simintov, a watan Agusta.

Ƙungiyarsa ta taimaki ‘yan mata da yawa na ƙaramar ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar, inda suka bar ƙasar.

Da yawa daga cikin ‘yan wasan – masu shekara 13 zuwa 19 – sun samu izinin shiga Birtaniya bayan sun shafe makonni a Pakistan.

‘Yan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar mata sun fice daga Afghanistan a watan Satumba

“Ƙungiyoyi da dama suna ta tuntuɓar mu – mutane na kira na da tsakar dare suna kuka suna cewa ‘malam ka taimake ni rayuwata tanba cikin haɗari’.

“Ina murna duk lokacin da na taimaka wa wasu amma kuma abin baƙin ciki ne duk da haka – ba komai nake iya yi ba.”

‘Sun fitar da ni cikin kwana ɗaya’

Ɗaya daga waɗanda Margaretten ya taimaka wa akwai Fareeda (ba sunanta na gaskiya ba ne), wata mai fafutika da ke kare haƙƙin mata da yara.

“Lokacin da Taliban ta ƙwace mulki na rasa komai,” a cewar mai shekara 25 ɗin. “Burikana da ‘yancina; ba zan iya fita waje ba, ba zan iya zuwa aiki ko jami’a ba – na rasa kai na”.

Ta ce ta yi “fafutika da kujiba-kujiba” kan kare haƙƙoƙi sannan dawowar Taliban kan karagar mulki ya girgiza ta.

“Na shirya zanga-zanga domin mu yi kira ga Taliban kan su ƙyale mana ‘yancinmu,” in ji Fareeda.

Fareeda ta yi amfani da shafukan zumunta domin nuna hotunan zanga-zangar.

Sai dai an yi amfani da hotunan an gano inda take.

Saboda jin tsoron abin da ka iya faruwa, ta gudu kuma ta nemi tallafi a wajen ‘yan ƙungiyar Rabbi Margaretten da ke ƙasar.

“Sun fitar da ni da dangina gaba ɗaya daga Afghanistan cikin awa 24,” in ji ta, tana mai ƙarawa da cewa: “Na yi farin ciki matuƙa.”

A lokacin da Taliban ke matsawa wajen ƙwace mulki, Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi gargaɗin cewa ƙungiyar na bin sahun mutanen da suka yi wa gwamnatocin ƙasashen waje aiki da kuma tsohuwar gwamnati.

Aalem (ba sunansa na gaskiya ba ne), tsohon tafinta ne da ya nemi tallafin Rabbi ta hanyar mutanensa.

Ya ce tun bai kai shekara 20 ba ya zama tafinta a 2003 lokacin gwamnatin Shugaba George W. Bush.

Yanzu da ya kai shekara 36, ya ce yana fargabar halin da ƙasarsa za ta shiga saboda haka ya fice daga cikinta. “Ina cikin masu fafutikar da suka tsere. Sauyin gwamnati ya firgita ni. Lamarin yana da haɗari sosai ga tafintoci – yanzu mutum ba zai iya zama a Afghanistan ba.”

A kwanakin da Taliban ta ƙwace iko da Kabul, jiragen Amurka da na ƙawayenta sun kwashe fiye da mutum 123,000 daga Afghanistan – duk da cewa babu tabbacin yawan ainahin ‘yan ƙasar daga cikinsu.

Har yanzu dubban mutane na yunƙurin barin ƙasar a kullum. Rabbi Margaretten ya ce zai ci gaba da taimaka musu “iya bakin iyawarsa”.

-Source:BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.