Afghanistan: Harin bam ya hallaka mutum 16 a Masallacin Juma’a

A ƙalla mutum 16 ne suka mutu yayin da 32 suka jikkata bayan da bam ya tashi a wani masallacin mabiya Shia yayin da ake gabatar da Sallar Juma’a a birnin Kandahar na Afghanistan.

Hotunan cikin masallacin na Iman Bargah sun nuna yadda tagogi suka farfashe sannan ga gawarwaki a zube birjik a ƙasa da kuma wasu masu ibadar da ke ƙoƙarin taimakon waɗanda suka jikkata.

Har yanzu ba a san abin da ya jawo tashin bam din ba, amma ana tsammanin aikin ƙunar baƙin wake ne.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya ji ƙarar fashewa har sau uku – daga ainihin ƙofar shiga, inda mutane ke alwala.

Masallacin cike yake da mutane a lokacin da bam din ya tashi kuma a ƙalla motocin ɗaukar marassa lafiya 15 ne suka je wajen.

Dakarun Taliban na musamman sun killace wajen sun kuma umarci mutane da su ba da taimakon jini ga marassa lafiyan, a cewar rahotannin Reuters.

Wakilin BBC a Secunder Kermani ya ce ƙungiyar IS-K, wani sashe na ƙungiyar IS ce ake zaton ta jai harin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ma an kai wani harin ƙunar baƙin wake wani masallacin ƴan Shia a birnin Kunduz da ke arewacin ƙasar inda mutum 50 suka mutu, wanda shi ne hari mafi muni da aka kai a ƙasar tun bayan tafiyar dakarun Amurka a ƙarshen watan Agusta.

Ƙungiyar IS-K ita ce mafi tsanani cikin dukkan ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya da suke Afghanistan, kuma tana adawa da gwamnatin Taliban.

Taliban ta ƙwace iko da Afghanistan bayan da dakarun ƙasashen waje suka janye daga ƙasar a ƙarshen watan Agusta bayan yarjejeniyar da aka cimma da Amurkan.

An yi hakan ne bayan shafe shekara 20 da dakarun Amurka suka yi a ƙasar inda suka kifar da gwamnatin Taliban a 2001.

-Source:BBCHausa-

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.