Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

‘Yan bindiga sun hallaka mutum shida a wajen gangamin yaƙin neman zaɓe a Anambra

Aƙalla mutum shida sun mutu a wani harin ‘yan bindiga a kudu maso gabashin jihar Anambran Najeriya.

An kai harin ne kan ayarin masu gangamin yaƙin neman zaben ranar 6 ga watan Nuwamba da ke tafe.

Mutane sun rasa rayukansu a musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga, sannan akwai da dama da suka jikkata a ɓarin-wutar da aka shafe sama da sa’a biyu a wata karamar hukuma.

Gwamna Willie Obiano na cikin mutanen da harin ya ritsa da su.

A watan da ya gabata ‘yan sanda suka rawaito cewa za su tura helikwafta shida domin taimakawa jami’an tsaro gabannin zaben da ke tafe a wata mai zuwa.


An yankewa ɗan uwan Abdelaziz Bouteflika hukuncin shekara biyu

An yanke wa ɗan uwan marigayi shugaban Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyu, bayan samun shi da laifin yi wa ɓangaren shari’a katsalandan.

An yanke wa Sa’id Bouteflika hukuncin ne tare da tsohon ministan shari’ar kasar Tayeb Louh, da wani ɗan kasuwa Ali Haddad, wanda shi kuma zai shafe shekaru 8 a kurkukun.

An tsare dukkan mutanen ukun ne bayan tilasta wa Abdelaziz Bouteflika sauka daga mukaminsa a shekarar 2019.

Daga bisani dai tsohon shugaban kasar ya rasu a watan da ya gabata, bayan shafe shekaru takwas yana fama da rashin lafiya.


EFCC ta ce shugabannin fansho na karkatar da kuɗaɗen jama’a a Najeriya

Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce shugabannin kamfanonin fansho na karkatar da bilyoyin kudaden mutane a Najeriya.

Ya shaida hakan ne a taron kwanaki biyu da ya ke halartar kan kawar da rashawa a tara kuɗaɗen fansho a Najeriya.

Bawa ya ce EFCC da ke yaƙar rashawa tana sane da irin aika-aika da ake aikatawa da kuɗaɗen fanshon mutane.

A cewarsa bincikensu ya nuna musu yada ake tafka rashawa a fanin fansho wanda hakan abin kunya ne ga kasa.

Ya kuma shaida cewa gwamnati na duba batun domin ganin ta samar da mafita da hukunta masu tauye hakkin mutane.

Kada Ku Rasa Wani Labari

Subscribe to our newsletter below and never miss the latest News Updates.